Yadda Auyo take da yaddah manyan Abin al’ajabi ya faru

KASANCEWATA A GIDAN KATEKO

Gidan kateko babban gida neh kamar yaddah na fada a baya gidane da yake da bangare da dama cikinsa amma ni a bangaren gidan su alhaji danladi auyo nake kuma mah bangaren mahaifiyarsa nake kunsan sune masu kudi kuma sune duk auyo na sansu amma kada mai karatu ya fahimci cewa na dauki bangare na masu kudi.


Babana shine aminin wannan mai kudi wato danladi auyo domin tun suna Makaranta, Makarantar su daya a T.C hadejia nan suka hadu bayan yayi arzikin sah kuma allah ya kara hadasu babana ya dawo bangaren sah yake kama masa wani bangaren a aiyukan sah sannan kuma duk abin da ya tashi a auyo ko kano to mahaifina yana cikin komai nasa.

haka suke rayuwarsu harma takai cewa danladi auyo yakai aminin babanmu na gaske,domin ya nuna masa soyayyah kamar dan uwansa na jini domin babana yafi wani dan uwansa be ma na jini a wajan danladi,
Komai ya tashi ko kana ganin danladi ko kana bukatar kayansa ko yama alkawari toh fah sai dai yace maka kaje kaga karda wato mahaifina domin shine zai baka shi kuma zai baka bayan wani lokaci kuma yasa a yi lissafi a biyashi kudin sah.

Danladi yana son babana sosai danladi idan yaga cewa akwai wani abu da babana zai sami kudi toh a lokacin neh zai yi kokari ya ture wanda ya dora da farko yasa mahaifina domin shi ya sami kudin.

TA YAYA NA ZAMA DAN GIDA

Nazama Dan gida sabo da wata rana bazan taba mantawa bah muna da makota a gidan mu na yayari dake nan hadejia muna masa lakabi da gidan azimin haruna suma mutanen auyo neh a wani gari ana cewa Makerayi to wannan shine farkon zuwana auyo sai su azimi suka ceh zasuje Makerayi bikin aure, shine babana yace zai kaisu kafin kace mai nace zan bisu auyo din zuwa garin nasu, wannan dalilin yasa na fara zuwa auyo kafin mu karasa sai ya karasa ratsa damu auyo wajan mahaifar danladi domin mu gaida tah sannan mu wuce.

Awannan lokacin neh fah muna zuwa a ka karbemu hannu biyu,amma a gaskiya matar nan ko nace mahaifarsa wato danladi auyo ya sami mahaifina mai mutumci,karamci,da kuma darajanta mutum domin daga Wannan ranar ta tambayeni sunana nace.

 

Muhammad tace babana kenan daga nan na koma sunana a gidan babana domin bata kara kirana bah kwata kwata, domin wai sunan muhaifinta nake da shi.

 

Bayan nan ko nace shine karo na na farko na zuwana gidan kateko dake auyo sannan muka ci abinci muka sha fura sannan hajiya ta bamu nama daga nan abba yace mu tafi ya karasa damu wannan garin da yake kusa da garin wato garin su azumi bazan manta ba lokacin damu da su iya maimuna, Asabe, alhaji, babangida da kuma ni, haka abba ya kyalemu a wannan kauyen mu a sunan munzo biki wajan biki.

 

Makerayi garine shide ba za’a ce masa babban gari bah sai dai ace masa karamin gari kawai dai kauye neh,sannan kuma suma suna noman shinkafa sosai domin suma shine abin do garinsu wajan nema,bayan nan kuma sai kiwo.

 

YA KWANA YA KASANCE A MAKERAYI.

Na kwana da yawa wajan kwanan mu biyar a wannan garin domin biki ranar ko nace wannan lokacin nakai kwana shida kuma shine karo na nah farko na kwanan kauye bayan haka kuma amma garin a kwai dubino mai kyau sannan bayan dubi no sai rijiyoyi na diban ruwa a garin wanda suke diban ruwa domin aiyukansu na yau da kullum, a takaice dai duk lokacin da muka dawo hadejia a kallah ban kara zuwa wannan garin bah sai bayan kusan shekara goma sha bakwai tukunnah na je dani da alhaji zuwa gona damin inaso nayi noma a wajan bayan haka wannan ya taimakamin kwarai da gaske amma daga karshe kawu.

Babannan bai sama min bah haka na shekara ina da kudi amma na kiyin noma ko sau daya wannan shine alakata ta farko da gidan kateko dake auyo ko nace gidan su danladi auyo, daga wannan ahekara sai nayi aboki a gidan mai suna Abubakar garba abubakar wato bala aboki na musamman sannan kuma amini na a duniya domin bala shine sanadiyata ta zuwa gidan kateko harma nakai yadda nakai a matsayina na makusanci ga wannan dangin domin yanzu nakai wani bangare a gidan domin tamkar dan gida haka nake a wajansu kuma tamkar sune suka haifeni domin kauna.

 

YADDA AKE NOMAN KANKANA A KASAR AUYO DA SIRRINTA

YADDA AKE NOMAN SHINKAFA A AUYO LOCAL GOVERNMENT JIGAWA STATE

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*