Wani Babban Gida A Auyo Local Government Jigawa state.

ALAKATA DA GIDAN KATEKO

 


Gidan kateko gidane kamar yaddah ko wane gida yake a kasar hausa amma Wannan gidan gidane babban gida waddah a kalla zaka samu mutane da iyalansu kimanin guda goma ko sama da haka amma da zarar kaji haka gidane a karkara.

Wannan gidan yana Auyo local government dake jigawa wanda suna dayah daga cikin manyan gida a karamar hukumar ta auyo sannan kuma gidane da yake da yawan mutane sama da dari biyu yayansu da matansu bama’a sa sa jikokinsu a cikin lisaafi suna zaune a garin suna ta noma da dabarun duniya wanda bazakace ta Yaya za’a rufawa kai asiri.

Cikin ikon Allah sai wani dansu mai suna danladi ya fiddah zakka ki nace allah ya zaboshi cikin yan uwansa ya masa arziki mai yawa ba karami bah domin kuwa har sai da yayi shura sosai cikin mutanen jugawa, Lagos dama kasa baki dayah.

TA YAYA YA FARA?

Da farko sunansa na yanka Muhammad Garba wanda ake masa da lakabi da Danladi Auyo,ya fara karatun primary anan garin auyo sannan ya kammala yayi karatun gaba da primary sannan neh fah bayan ya gama sai ya tafi fantai hadejia domin ci gaba da karatunsa nah secondary school a nan hadejia amma kuma Makarantar Makarantar kwana ceh ba jeka ka dawo bace.

A Nan neh ya gamu da mutane daban daban inda ya gamu da abokan arziki wanda har yanzu suna tare kuma sune aminan sa na kusa wannan ba karamin nasara bace a rayuwa ka yi Makarantar kwana domin tana koyar da abubuwa sosai kamar su tar’biyyah sannin abubuwan da ya kamata dama iyah Zama da mutane.

YA BANGAREN KASUWANCI YAKE

Bangaren neman kudi kuwa bangarene na musamman a rayuwarsa,Wanda ya farah neman kudin sa a auyo local government inda ya fara da kasuwar buga bulon kasa ma’ana dai bulan kasa yake yi yana sayarwa nan daga bisani yayi bulan kasar a bayan wani ruwa a auyo mai suna ramin shadai dake daya daga cikin ruwayen dake cikin garin auyo domin allah ya albarkaci auyo da ruwa daban daban.

Haka yake daga nan sai yayi tunanin ya yi bulan kasa ya tara kudi ya tafi Lagos neman kudi domin bulan kasa sai a hankali,bayan Wannan tunani da yayi sai ya tara bulo yana sayarwa nan neh fah ya maida himma wajan tara kudi domin yana da abin da yake hanga ko wani abu dake cikin zuciyarsa.

 

Bayan ya samu kudinsa na mota da kuma gujiri na tafiyarsa kasar ikko ko nace Lagos State,bayan dan lokaci ya gama shirinsa tsaf ya fadama iyayensa ga kudirinsa na tafiyah neman kudi zuwa jahar Lagos dake kudancin nigeria nan bayan dogon tunani da kumah fahimtar himmarsa wajan neman na kansa sai suka amince abinka da gidan malamai suka zauna suka ta add’uar neman sa’a a gareshi sannan ya kama hanya zuwa jahar Lagos dake kudancin kasar nan.

SHIGA JAHAR LAGOS DAKE KUDANCIN KASAR NAN.

Ya shiga jahar Lagos dake kudancin kasar nan da niyar ya fara wanke takalmi da kuma gyaran takalmi inda da ga saukarsa ya fantsama wajan neman kudin sa sannan ya maida shimma wajan tara kudinsa nan kafin kace mene allah ya sah albarka cikin neman sah, sannan kuma ya tara kudinsa ko idan lokacin ya sami mutane masu tahowa a basu sako ko kuma yama taho domin duba gida inda idan yazo yakan yiwa yan’uwa da abokan arziki abubuwan ban mamaki.

KASANCEWARSA SHIGA KASUWAR CANJI

Ya shiga kasuwar saye da sayarwa ta canji neh sabo da wani hamshakin dan kasuwar kuma attajiri a harkar canjin a kasuwar canjin kasar nan, Wanda shine bahaushe na farko a cikin garin Lagos ko ace kasa baki daya da ya fara canji a Wannan lokacin wato alhaji yunusa director Allah yaji kansa da rahama yasa aljannah itace makomarsa a garshi damu baki dayah.

 

wannan mutumin alhaji yunusa director mutumin auyo neh kuma ya dauko alhaji dan’idi kuma dansane domin shima dan auyo din neh kuma dama yayi karatu wannan ya taimaka masa matuka wajan zama a office din canji.

 

Bayan diban lokaci da fahimtar kasuwar yaddah take nan neh shima danladi ya samu kudi mai yawa sannan ya farah tarashi sosai daga nan kuma ya farah zama mai dan tarin dukiya wanda wannan kasuwar ta canji ta ci gaba da kawo masa alheri kamar da bakin kwarya kasan duk abin da Allah ya nufa yace ya faru yanzu zakaga kamar wasa ya faru.

 

SHAHARARSA A KASUWAR DA YAR’BAWA

Cikin ikon Allah kafin kace mene zuwa wani lokacin samun kudin sah sai girma yake sosai kamar wasa yaddah shima kansa har abin mamaki yake amma Sabi da a al’amarin allah ba’a mamaki,dalilin mamakin Wannan yawan kudin shine duba da karancin shekarunsa da yake fama dasu amma kasan abin allah ba ruwansa da kai tsoho neh ko yaro idan allah yaso da yamaka ni’imah alhamdulillah ya samu.

Kunsan dai inda jahar Lagos take da yaruba, iyarai da dai kabilu daban da haka wannan bawan allah ya zauna dasu ya koyi halayansu da zuriya da kuma hakuri yake kasuwanci dasu har suka aminta dashi sosai,wannan ya taimaka masa matuka yazo ya sami abin duniya ta wannan bangaren domin sai kun fahimci su wane su zaka iyah kasuwa dasu gaba ki dayah.

Yaddah Ake Sarrafa Masara Ta Koma Garin Biski Da Surfaffiyah A Kasuwar hadejia

Yadda Ake Sarrafa Masara ta koma Garin Yar’funtuwa A KASAR Hadejia.

 

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*