Babar Abota tana hada kan Al’umma Saurari Abotar Abubakar da Muhammad

YADDA KUMA NA ZAMA DAN AUYO SABO DA ABUBAKAR GARBA ABUBAKAR.

Abubakar garba Abubakar abokina neh kuma yayana neh domin wani bangarene na rayuwata,zuwana auyo na biyu shine muka hadu da bala,nasan duk nima bankai shekara goma bah amma shima baiyi ko sha uku ko kusan sama amma bansan shekarunsa bah kwata kwata,bayan haka,muka tasi tare dashi cikin son juna da shakuwa sannan zakaga bala yazo wajena hadejia sannan nima daga baya sai nima naje masa auyo gidan kateko ma’ana gidansu kenan wato family house kenan.

 

Bayan wannan kuma bala wani mutum ne mai son jama’a da yawan abokai,bayan haka bazan taba mantawa bah a auyo na fara sanin mece budurwa mah a rayuwa ta bayan haka a auyo nasan wani wasa na al’ada mai suna wasan mishal wanda ni tun da nake a auyo kawai nasan ana wannan wasan.

 

TA YAYA NASAN WAI MUTUM YAYI BUDURWA.

Na fara sanin mutum wai yayi budurwa a auyo domin bazan manta bah muna yara wata rana naje auyo wajan bala hutu sai kawai yace min yana da budurwa nazo naje na rakashi zai ganta zasuyi magana da ita sannan kuma ya nunamin itah domin na santa,kafin kace mene daman yana da wani keke wanda aka saya masa ya dauke ni ai sai gudu muna gaggawa wai zanje wajan budurwa sai kawai naci taka ji kake tas a kasa a keyata domin hakan ya taso ko nace ya faru sakamakon tashin tsaye da kuma hawa keken babangida na fado,gogan naka kuma baima san na fado kasa bah domin kawai gudu yake sai da aka ce masa na fado tukunnah ya dawo ya saukeni kasan abinka da yarinta wanda ka fadi mah sabi da burgewa mah sai ka nuna bakaji komai bah,haka ya daukeni sai wata unguwa ana ce mata unguwar makada gidan wani mutum ana ce masa baki kamsila shine mahaifin wannan budurwar bala sannan bala ya tura a kirawo ta zo.

 


Bayan tazo nasan sunanta muka gaisa ashe sunanta mamawo daga nan na fara jin ya ake soyayyah daman haka ake soyayyah,sai kuma nake tambayar kaina haka wannan garin yake sannan kuma sai bazan taba mantawa da wani wasan mishal da shine wasa na farko da na fara kula mace ko wani abu domin wasane na gargajiya kuma wasane wanda yake da amfani kuma na fara wasan mishal ne a garin auyo sama da shekara goma sha lokacin muna zaune da bala sai bala yace zasuyi wasan mishal nace wannan kuma wane wasa neh nan naje naga yasu bala suka aiwatar da nasu sannan kuma nata fahimtar sah domin na fahimta al’ada ce kuma mai cike da mahimmanci da kuma nuna abu mai amfani ga rayuwar matasa.

 

Bara na fayyace muku ya na gudanar da wasan mishal dina a karon farko a garin auyo.Domin ka fahimci ya wannan wasan yake,domin idan son samune ba don tarbiyyah tah lalace bah da naso ko wane gari sun sashi domin amfanin da yake da kuma yaddah abubuwan suke shakatarwa, wa’azantarwa da dai sauransu domin ace baku da al’ada to kamar baku da asali neh a kasar hausa, yanzu misali mu dauki kasar hadejia ko kuma nace mu dauki karamar hukumar hadejia tun da na taso banga wata kyakyawar al’ada da ake gudanar wa bah sai hawan sallah ko nace hawan doki domin kamar hadejia bah abin da suka iyah sai hawan doki.

 

Kuma gasu sarakai masu ji da kansu domin kowa mah sarkine a hadejia¬† domin kasan su sarakai dole sai da abin al’ada amma kuma fah ina tunanin duk wata al’ada ai tana fada amma sabo da mu bama tare dasu bamu ba su kuma bazamu san ya abun nasu yake bah domin kunsan wallahi ni bana bukatar sarauta a zuciyata¬† domin ina da mutumin da ya dorani akan doki na farko wato kawu garba likacin da muna yara muka hadu dashi mukace muna son mu hau doki sannan kuma bama dokin bah ina so na koya kawai kunsan zuwa mukayi murin doki na wani mutum an sauko daga kan doki.

 

Baka dorani aka jama wuyan dokin aka jah daga nan neh fah hawana na farko a duniya, sannan kuma ban kara hawa doki bah sai bayan wajan shekara goma sha sannan a auyo na hau kan doki,sabi da rashin tsoro irin nawa kawai nahau nace na iyah ana sakina na dire na gudu dikin kuwa ya tashi sama domin naja linzamin dakyau haji zafi wanan dee shine hawana na farko kan doki na ajiye maganar wannan shine ta kaitaccen labari a kan auyo sai kuma mu duba ya ake wannan wasa na mishal domin mai karatu ya fahimta.

YADDA AKE NOMAN SHINKAFA A AUYO LOCAL GOVERNMENT JIGAWA STATE

INNALILLAHI, WATA MATA, TABAY YANA YADDA TAKAMA MAHAIFIYAR TA TANA ZINAH DA BOKA.

 

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*