Yaddah Ake Sarrafa Masara Ta Koma Garin Biski Da Surfaffiyah A Kasuwar hadejia

YADDA AKE SARRAFA MASARA TA KOMA SURFAFFIYAH

Masara surfaffiyah masarace waddah ake sarrafawa ta koma gari,ba wahala cikin sarrafa Wannan masarar,Amma nayi amfani na rubuta yaddah ake sarrafawa.

Masara surfaffiyah kawai mutum zai Sami masarar sah Koda buhu nawace zai kaita wajan masu injin surfe Wanda Wannan injin surfen zai surfata ta yaddah zai rabata da dusa da Kuma ai nashin masarar toh sai a dauki ainashin masarar a kaita injin nika Wannan lokacin bah jikata za’ayi bah kawai daga surfe sai asah masu shika su sheketa sai kawai a n ka.

 

Wannan itace maaara surfaffiyah amma na zanta da wasu yan kasuwa suna nunamin cewa ita surfaffiyah masara bata da riba gabaki dayah kawai domin an rage mata yawa,amma fah sai kuma dadi da take da itah ba yawa wannan kenan a takaicen takaitawa.

 

GARIN BISKI NA MASARA.


Garin biski na masara, Masara ce waddah ake sarrafawa ta koma biskin masara ko wasu suce bira biskon masara wannan wata hanyace da ake sarrafa masara ta koma kamar tsaki amma ba taaki bane buski neh na garin masara.

 

Ana sarrafawa tane ta hanyar wani inji da ake kiransa da suna injin biski wanda shima daban yake da wancan injin nah surfe,shi kawai yana mayar da masarar neh zuwa biski amma da dusa a cikin garin,sai an hada kawai sai a sami rariya waddah ake hada tah kawai sabo da tankade,waddah wannan rariyar gaba daya anayinta neh saboda Wannan biskin domin rariya ceh ba irin normal rariya bah ma’ana irin tah gida aa Wannan wata irin rariya ceh waddah idan zakayi tankaden sai ta dau wajan kwano goma na garin.

 

Bayan kuma an gama tankaden sai a sami buhu a zuba ko kuma a dauko kwanan awu ana auna kwano kwano har guda arba’in domin cikarsa baki dayah,wannan shine zai baka damar kasan kwano nawa ka rika na riba,amma maganar gaskiya garin biski yana da riba sosai tah yaddah mutum baya tunani,sannan sai a kawo shi doran kasuwa a sayar dashi buhu buhu ko awu awu ma’ana kwano kwano.

 

YADDAH AKE SARRAFA MASARA ZUWA GARIN DATSA.


Yaddah ake sarrafawa masara ta koma garin datsa wannan shine yake da sauki duk cikin yaddah ake sarrafawar domin sarrafawa yana taimakawa da yawa amma garin datsa tafi shiga a doran kasuwa sabi da tafi karamin kudi sannan kuma mutanen da suke sayan tah sunfi yawa Sabi da rashin kudin da ake fama da shi a wannan zamanin.

 

Sarrafawar masara zuwa garin datsa kawai akan dauki masara a kaita inji bah wando kawai a zuba mata, shikenan sai garin datsa ya fito kawai a zubashi a buhu sai kawai mutane su saya suje su tuke tuwonsu a gidajen su suci da iyalai baki dayah.

 

A yanzu kasuwar da muke fama da itah matsalar da ta shafi masara shine rashin karkarfan jarin da mutum zai juya domin mutum ya sami wani abun da zai juya, a sannan kumah a harkar masara abin da bazan taba mantawa bah shine Mai gidana alhaji dan’idi kanin mahaifiyata shine mutum na farko da yazo ya koyamin harkar kasuwar masara waddah har’ila yau inah alfahari be da wannan kasuwar domin tah taimakamin kwarai da gaske bah da wasa bah,bayan haka inah da babban Manager kuma mai gida a harkar masara wato maigida babani domin har gah Allah babani bani kadai bah mah muna da yawa babani ya taimaka Mana wajan sanin masara,sanin inji da dai sauransu.

 

Ba zantaba mantawa bah lokacin muna yara,lokacin muna yaran inji sai kawai kaga muna ta rigar buhun masara wanda duk buhu dayah idan ka gyarah sai a biyaka naira hamsin wannan lokacin amma fah hanunka zai fada maka,Wanda idan ka dade kanayi sai kanta tabi ta fitomah a hannu wannan yana daya daga cikin aikin wahala da mukayi lokacin muna yaran shago ko nace kamfani,

Bayan haka kuma sai mai gidana wato bayaro azamu wanda har yanzu muna tare dashi a kasuwar cikin garin hadejia ana tah fama,bayaro mutumin kirki neh wanda ina mai mar add’uar Allah yaci gaba da buda masa duniya da lahira, waddah gaskiya bayaro yana da son kai nasane ba nasa bane kawai ka samu kuma bayaro yakan baka kayah kaje ka dauka sai kah aikata kayi abinka sannan zai wai wayeka kumah duk da haka ko kallonka ba zai kara yi bah akan hakan sai dai kawai in kaga dama ka kai masa kudinsa.

 

YADDA AKE NOMAN KANKANA A KASAR AUYO DA SIRRINTA

13 States Get New Commissioners of Police.

Access Bank Advance Africa Scholarship Program

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*