Yadda Ake Sarrafa Masara ta koma Garin Yar’funtuwa A KASAR Hadejia.

YADDA AKE SARRAFA GARIN MASARA YA KOMA YAR’ FUNTUWA.

Yadda ake noman masara a kasar auyo,masara a bayan shekaran da tah gabata bah da dadewa bah masara bah tah ciyiwa sosai a kasar hausa duba da yawan abunci da Kuma saukin samu a ko inah,Wanda dah samun kudin sayan kayan abincin da sauki koma bayan yanzu.

Yanzu kuwa masara ta Zama wani bangare ko nace gimshikin cikin abincin da mutane suke ci na yau da kullum,sannan masara bata taaya nan bah sai da darajar tah ta Kara dinka kanta kimanin kaso 4o% akan kudinta na yaddah aka santa,sannan hakan ya kara zawo yawan monomanta a fadin kasar waddah sun yawaita da kimanin 10%, Wannan yana da mahimmanci kwarai da gaske sai dai kuma hakan ya kara kawo mana tsadar duk wani na’in abinci da ya danganci masara,misalin wadannan abu buwa sun hada da kwai Wanda yanzu a doran kasuwa yakai kimanin #800 ga ko wanne kiret a kasuwa.

 

Bayan haka masara bata tsaya a nan bah ta shiga cikin gidajen mutane sosai domin a yanzu tah zama wata gagari talaka duk da ana ganinta a komah bayah cikin kayan abinci, sannan masara ta kara samar wa matasa aikin yi ta bangaren sana’a waddah hakan cigaban kasa neh, yadda ake sarrafa ta hanya daban daban sun hada kamar haka:

  • Yar’funtuwa
  • Surfaffiyah
  • Tsaba
  • Garin biski

 

YADDAH AKE MAYAR DA ITA YAR’FUNTUWA

Masara ana sarrafa tah ta koma wani dau’in gari mai haske da gardi, Wannan garin masarar ana sarrafashi ya bad rukunin wadannan garin da muka ambata a samah Kuma ta hanya Mai sauki,da farko dai mutum zai sayo marar sah Koda buhu biyu (2) ceh yama Farah da itah.

 


Da farko zai kaita wajen surfe, ma’ana injin surfe domin surfa Wannan masarar tah mutum,bayan an jika tah sai a zuba a cikin injin surfen, bayan nan sai mutum ya sheketa may be mutum ya kira masu shika su gyara ko kumah ya samu fanka ya sheke a gabar fankar tunda tah samar masa da iskar da zata taimaka masa ya cire dusar da take cikin.

 

Bayan an gama raba tsabar masarar da dusa sai kumah ya nemo duro nah mai ya zuba tah a ciki,amma da farko za’a zuba ruwa a ciki yazo iya kar bakinta ko kumah ya cika duron sai a daibo tah ana zubawa a cikin duron.

Bayan an gama zuba wa sai kumah azo a kara cire dusar da taki ciruwa cikin shikar,sannan a kyaketa tsawon kwana 2 ko Awa 24 dake cikin yini,sannan kumah sai a taafeta daga cikin ruwan amma kafin nan kumah sai an samo ruwa da faffen duro wanda za’ana wanke tah a ciki domin zakaji dan gumamar tah da danko wannan itace alamar masarar taci zata iyah komawa wannan garin a sannan neh mutum zai samo tamfol ya shinfida a fili wanda zai sah tasha iska na tsawon kamar awa 2 amma sai ana juyata tukunnah zata nuku.

 

Daga nan za’a dauketa zuwa injin da ake nuka ma’ana azo a sakata a inji Mai wando ko kumah barar wando,ana gamah nikan ko ana nikawa ana kaita can wajan da aka tanadar domin shanyar wannan masarar,ko muce nikyakiyar masarar daga Nan fah ta kusa komawa yar’funtuwa da ake bayani a kanta.

 

Bayan tasha iska sai a sami masu kumah tankade a manyan rariya da ake amfani da ita zata tacemaka guntuwar dusar da bata fitah bah cikin garin,sannan kumah sai a nemo laida,buhu da zare da musullah domin zuba yar’funtuwa cikin buhu domin tah zama garin yar’funtuwa da ake bayani akai.

 

Wannan shine garin yar’funtuwa daga nan kuna sai a samo masaya a Wannan lokacin garin masarar yana shiga gida da kauye wanda hakan yana taimaka mAh wadanda suke da kana nan masu hali,wasu zaka gah sunzo sayan garin masarar wasu buhu,wasu kumah kwano¬† wasu kumah sun kan sayi rabin kwano ya danganta.

 

Manyan manyan dilolin Wannan masara a kasuwar hadejia sune irin su alhaji Dan Idi ,Kila hadejia da Kuma Mai gida bayero, wadanda muke dasu a kasar hadejia baki dayah wanda a kallah zaka’samu ma’aikata kimanin samah da mutum dari da hamsin da suke samun moriyar wannan sa na’ar masarar domin nagani mutane da yawa sun kafu sun ginu da yawa a kan harkar waddah wasu itace cinsu itace shansu baki dayah.

 

World Bank Group Fellowship Program 2021 Scholarship

Yadda mumunan hatsarin mota ya rutsa da wasu mutane suka rayu

 

Labarin wata soyayyah Mai ban sha’awa ta Bili Usman Mai nasara

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*