YADDA AKE NOMAN SHINKAFA A AUYO LOCAL GOVERNMENT JIGAWA STATE

 

 

LABARIN YADDA AKE NO MAN SHINKAFA A AUYO LOCAK GOVERNMENT JIGAWA STATE

Auyo local government Karamar hukuma ce dake cikin jahar jigawa waddah tayi iyaka ta yamma da kafin Hausa local government Wannan tayi iyaka da hadejia ta gabas, ta arewa kuwa tayi iyaka da kaugama local government, tana da mazabu guda goma.
Wadanda suka hada da Auyo, gamafuai, gamaarka, unik, gatafa, kafur, zidir, hadiyau, adaha, ganuwar kuka, wadannan sune suka hadu suka kafa Auyo local government area.

 


Sannan Auyo Karamar hukumace waddah take da albarkattu na karkashin kasa da ma’adainai, Amma babbar albarka da Allah ya ajiye musu shine noman shinkafa,
Noman shinkafa nomane da akan yishi Wanda ya Shafi yaddah ake yinsa kala kala waddah wasu al’ummar sukan ceh ta rabu Kashi biyu da noman shinkafa ta watse da Kuma ta dashe.

NOMAN SHINKAFA YAR WATSI

 


Noman shinkafa yar’watse nomane da ake yinsa,Wanda manomi zaizo ya ya gyarah gonarsa ma’ana zaizo yayi haro na gonar sannan ya samu irin shinkafa shanshera ma’ana waddah bah a fitar daga kwanso bah sai a samo taking waddah za’a hada da shinkafar wajan watsa shinkafar a Wannan filin da aka gyara domin Wannan noman yar’watsin.

Amma kafin a nemi wajan da za’a yi yar’watsin Dole a Sami wajan da ruwa yake taruwa ya Zama dai ruwan sama ko na kogi Yana taruwa a wajan ya cika wajan,sannan kafin ruwan ya shiga sai a watsa shinkafar da akayi miss dinta da takin zamani, bayan an watsata sai abi a binne tah da kasa amma binewar bah zan kasa bah,

 

Bayan an binneh irin a kasa idan da damah sai a zuba ruwa ma’ana ayi bayi na Dan wani lokacin ko kumah idan anyi ruwa ya zamah Yana jikata dakyau,sannan sai a barta idan Allah ya kawo ruwa shikenan zatabi ruwan ma’ana ruwan yana shiga shinkafar zatana tashi samah haka har ta girma da zarar ruwan ya gama shiga gonar sai shinkafar ta tsaya tayi Abu Mai kyau ma’ana kwaya Mai kyau sannan idan ruwa yaza sai azo a Yankee tah Abu guge tah wannan shine noman shinkafa Yar watsi a takaice.

SHINKAFA YAR DASHE

 


Shinkafa Yar dashe shinkaface waddah mutan Auyo gabaki dayah suke yinta Rani da damina,shinkafar dashe anayinta da farko za’a Farah gyara wajan ma’ana za ayi haro sannan kumah ayi levaling a gonar amfaninsa a daidaita fadin ganar kada can yayi tudu ko yayi kwari domin samun ruwa ya kwanta a ko inah Wanda zai bawa gindin shinkafar ya kasance da ruwa a jikinsa.

Sannan bayan haka sai a jiga gonar ko fadin gonar inda aka gyara domin dashen domin samun damar da za a samu a Sami dashen cikin sauki,

Wannan shine zai bawa irin shinkafar da aka dasa ya Kama gindinsa ma’ana ya ajiye jijiya a kasa ya Farah haihuwa, akan kirawo mutane yara ko manya a Basu irin shinkafar su dukuwa suna likata a ruwa har sai sun gama da ita.

Kuma dashen shinkafar akanso a ganshi kusa kusa domin na farko yawa, damar haihuwa da Kuma high humidity, Wanda zai tai maka mata ta girma ta haihu da yawa ta cika gonar, sannan sai azo a mata fisar kwayar ciyawa kunsan ciyawa na Bata komai ita ake nufi da (Unwanted plants).
Bayan kwana goma ko Sha hudu zai azi a zuba mata takin ta hanyar watsa Shi ta ko ina cikin inda shinkafar take ruwan da ke cikin shinkafar zai narkar da kwayar takin har ta zuki abincinta Amma takin ba ko wannane ake sa mata bah da farko ana sa mata (NPK).

Bayan Nan sai kuma a Sami kwana kamar goma a mata ciran ciyawa na farko kunsan Dole ayi ciran ciyawa domin barin ciyawa Yana kawowa babbar matsala sosai a gona,
Bayan ciran ciyawa sai aci gaba da Bata ruwa tana Sha sosai,sai kuma a dan tsagaita mata da ruwa amma bah ya kare bah aa kawai dan tarab tarab a cikinta domin Shan iskah shine zai Bata damar haihuwa kaji idan kazo yankan shinkafa kaji tana cika mah hannu sai dai kayi kamu biyu da itah, sannan sai azo a naimi taki na biyu azo a watsa mata Amma a Wannan lokacin bah NPK za’asah mata bah aa (Urea) za’a sa mata domin shine zai Bata damar you tsayi da Kuma fitar kan shinkafa gadar gadar.

Saka mata taki na biyu Yana da mahimmanci sosai Dan daga Wannan lokacin zaka ga shinkafar kah ta Farah duhu ko nace baki, Wannan shine alama zata Farah kunshi ko nace fitar da Kai (Zangaryar gwaya) tana tafe zaka gah ta Farah Kai can ma’ana jifa jifa sai kumah ko wacce a hankali tanayin Kai.

Sannan cikin ikon Allah bayan takai Wannan matakin zakaga ta Farah busawa ma’ana bushewa tana jah Kuma kan nata shine zai yi jah, sai a naimo wadan da zasu yanke tah da lauje su yanke su tare tah sai kumah a samu masu bugun shinkafa suzo suyi.

Facebook Fellowship Program for International Students 2021/2022

 

ABU DHABI UNIVERSITY FULLY-FUNDED SCHOLARSHIPS FOR INTERNATIONAL STUDENT2021/2022.

 

Khadija University majiya application form in to 2021/2022 Academic section.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*